FITSARIN FAQO 📚📖
page 3-4
Na tada kai na dubi kujerar faruq na tuna farkon saduwarmu da shi. Lokacin da na tafi aikin bautawa qasa a jihar Anambara muka hadu da shi , kungiyarmu 1 . Faruk irin mutanen nan ne masu tsananin surutu wadanda duk inda suka shigabdole a san dasu a wajen. Duk 'yan bautawa qasar da muke tare a masaukinmu NSUKKA sun san shi. Santalelen saurayi ne fari kuma ga kyakkyawan gashi da wani irin kwarjini na musamman . Sa'annan ya iya hulda da mutane . Allah ya yi masa tagomashi ; kowa yana sha'awar yayi aboki da shi tun bama dai 'yan mata ba.
Wata rana mun fito filin wasa sai shugaban 'kungiyarmu ya sanar da mu cewa za ayi gasar wasan kwaikwayo game da aikace aikacen 'yan bautawa qasa kuma ana neman wadanda zasu iya da kuma wanda zai taimaka a rubuta a kuma gabatar da shi. Ni ban taba rubuta wasan kwaikwayo ba amma na rubuta ' yan gajejjerun labarai da aka buga a jaridu da mujallu . Wannan sanarwa ta qara mini qaimi sai na daga hannu nayi gaba . Jim kadan sai naji an kaure da tafi . In waiwaya haka sai naga Faruq ya nufo mu da hannayensa cikin aljihun wata jaket dinsa sabuwar yayi. Da ya iso wurinmu ya dora hannuwansa a bisa kafadata yace "Allah ya sa dai kai ba injiniya ba ne". Na ta da kai na dubeshi . Ya yi murmushi nima na yi , don ganin ni ma na samu hanyar da zam kulla yace domin injiniyoyi ba su rubuta wani abin kirki na annashuwa . Duk tunaninsa a kan ginin gadoji da lantarki da injuna yake qarewa".
Na gaya masa ni ilimin siyasa na karanta a jamI'ar Ahmadu Bello Zaria . Sai ya miko mini hannu muka gaisa , yace "sunana Faruq Awwal, dan jarida ne ni amma nafi qarfi wajen tsara mujallu. A jami'ar Fourah Bay ta qasar Saliyo nayi karatu. Amma fa ni dan Najiriya ne gaba da baya.
Kafin sauran 'yan kungiyarmu su Ankara mun zama abokai. Shugaban Kungiyarmu ya fuskance mu yayi mana bayanin abubuwan da ake bukata . Mu kuma bamu 'bata lokaci ba muka duqafa sai da muka yi kimanin wata guda muna aiki tare ba dare ba rana muka tsara wasan muka kuma gabatar da shi cikin nasara. Kungiyarmu ce ta lashe gasar. Jaridu duk suka buga labarin gasar da sunayenmu , ita kuma mujallar 'yan bautar qasa ta buga tarihinmu . Daga nan fa muka qara shaquwa da Faruq muka zama 'yan uwan juna kowanne lokaci muna tare.
Cikin haka ne Faruq ya bani labarin iyayensa mahaifinsa wani shahararren dan kasuwa ne da ke zaune a saliyo . Kanuwarsa Jamila 'yar makarantace Free Town . Faruq yakan mini tadin ta, yakan ce ya tabbata jamila zata soni in taji cewa na tsani almubazzaranci da kudi , wanda yake ita ma halinta ne . Ya ce halinmu daya da ita kuma ya tabbata zamu so juna . Haka kuww aka yi kamar Faruq na duba . Saduwata da jamila ke da wuya soyayya ta qullu tsakninmu har muka yanke shawarar yin aure.
Na rigaya na gaya wa Faruq abin da nike da niyyar yi bayan aikin bautar qasa . Shi ma kuwa ya bayyana mini nufinsa na kafa kamfanin buga mujallu . Na dade ina nazarin yadda ilimi ke bunqasa a kasar Hausa . Hausawa da dama sun yaqi jahilci sun iya karatu da rubutun boko . Amma abin takaici duk da haka babu wata mujallah ta Hausa da wadannan dubban mutane zasu riqa karantawa akai akai . Nayi ta sha'awar ganjn wani mai kishi ya fara irin wannan mujallar , amma ina!, kowa na tuntuba sai ya zuqe . Hakika kam kasada ce babba mutum ya zuba jari a wata sabuwar harkar da bai san kanta ba sosai , sai dai ni na amince buga mujalla harka ce mai riba wacce zata iya sa mutum ya wadata cikin lokaci kankani kuma ya yi suna . Ni kam ban dauki harkar da wasa ba. Duk littafin da na yi karo da shi mai bayani game da harkar buga littattafai da mujallu sai na karance shi. Ta haka na ilimantu da harkaR buga littattafai , sai dai rashin jari shine babban abin takaici . Dole ne in hada kai da wani don samun isasshen kudin da irin wannan mujalla ke bukata . Da taimakon wani abokina wannan tattalin arziqi na sami qiyasi da zai isa da kuma na yawan ribar da za a iya ci . Da wannan bayanin na ciwo kan faruq ya yarda mu kafa kamfanin buga mujallar da muka sa wa Suna Arewa . Ba mu shekara biyu da farawa ba sai da muka kai ga muna buga kofe dubu ashirin da biyar a kowane wata.
Ina cikin wannan zun zurutun tunani sai naji kamar an kwankwasa kofa . Na daga mai na dubi kofa nace a raina "ina ma ace Faruq ne ya dawo ?" ko a da kofa ta bude sai na ga ashe Ngozi ce

0 comments:
Post a Comment