Home

Music

Video

Kannywood
Tags:

MANCHESTER UNITED TAYI SABON MAI HORARWA


Subscribe Our Channel

Kungiyar Manchester United ta bayyanar da tsohon dan wasanta wato Ole Gunner Solskjaer a matsayin wanda zai cigaba da lura da kungiyar har qarshen wannan kakar wasannin bayan korar da sukayiwa tsohon mai horar da kungiyar Jose Mourinho.


 Tsohon dan wasan gaban manchester United wato Ole Gunner Solskjaer zai dau ragamar ci horar da kungiyar har zuwa karshen wannan kakar wasannin a yayin da kungiya zata cigaba da neman Mai horar da kungiyar dindindin.


Shidai mourinho an koresa ne ranar talata r 18 ga watan disambar 2018 bayan kwashe shekara 2 da rabi a matsayin mai horar da kungiyar a filin wasan su na OLD TRAFFORD wanda yanzu haka suna mataki na 6 a gasar gida ta ingila inda akwai maki 19 tsakanin su da masu jan garamar teburin wato Liverpool.


Ole Gunner Solskjaer zai hadu da Mike Phelan a matsayin mai horar da kungiyar Manchester United.

Kungiyar Manchester United sun sanar da bawa Ole Gunner matsayin mai horar da kungiyar tasu ta shafinsu na yanar gixo inda suka fitar da wani bidiyo inda Solskjaer Da wasu manyan mutane na Manchester United suna murna a ranar talata.


Tsohon mai horar da Real Madrid da kuma Mai horar da kungiyar Tottenham Hotspur suna cikin jadawalin masu horarwar da Kungiyar Manchester United suke sa ran zasu kawo a sabon kakar wasanni masu zuwa.

Share this


0 comments:

Post a Comment

FG HAUSA | All Rights Are Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Designed By ASSALAPHY