*HUKUNCIN MAI JANABA DA YA YI ALWALA YA YI SALLAH YANA SANE*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum malam ina da tambaya, tambayar Itache::
Idan mutum yayi mafarki har maniyi yafita daga gabansa kuma gashi lokachin sallah Asuba yayi yana tsoron yin wanka a wannan lokachin sai yayi Alwala da ruwa a madadin yayi taimama yaje yayi sallah da wannan Alwala to malam minene hukunchin wannan sallah dayayi ? Kuma na dade ina aikata hakan yanzu yaya kenan?
Allah yaqarawa malam lafiya da tsoronsa.
*Amsa*
Wa alaikumus salam
Toh dan uwa salla dai batayi ba, idan ka tashi da janaba kuma bazaka iya taba ruwa ba saboda wani dalili sai ka dafa ruwan kayi wankan ka. Malamai na hujja da fadar Allah cikin suratun ma'idah aya ta 6, ga wanda bai samu ruwa ba ko akwai ruwan amma sanyi mai tsanani ya hanashi anfani da ruwan, ko zai iya kamuwa da rashin lafiya sana diyyar taba ruwan kuma babu abinda zai dafa ruwan suka ce sai yayi taimama don yin sallah, don fadar Allah cikin suratut tagabun 16, aduba: (Fathul baari 1/454,) da (fatawa bin Bazz 10/199-200)
Sannan kasan cewar ka dade kana aikata haka shari'a bazata tilasta maka rama sallolin dakayi abaya ba, don fadar Allah cikin suratul bakara 286, da Suratul Ahzaab 5, da hadisin Ibn Abbas wanda Ibn majaa da baihaki suka ruwaito manzon Allah SAW yace (lallai Allah ya daukewa al'ummata (laifin) kuskure da mantuwa da abinda aka tilasta musu akan sa).
Wallahu A'alam
*ENGR JAKSON

0 comments:
Post a Comment