Home

Music

Video

Kannywood
Tags:

KULLUM RANAR MASOYA CE A ADDININ MUSULINCI


Subscribe Our Channel

Bahaushe mutum ne mai tsananin rikon al`adunsa, kuma galibin Hausawa Musulmi ne, wadanda kunya da koyarwar addinin ke taka muhimmiyar rawa a harkokinsa na rayuwa.
A ranar Laraba ne ake bikin ranar masoya ta duniya; shin yaya Hausawa ke kallon wannan rana?
'Yan magana dai kan ce soyayya kogi ne, kuma idan ba ka sha to ka ratsa.
Don haka kamar sauran bil`adama, Hausawa masoya kan nuna zunzurutun kauna ga junansu, amma saboda al`adar kunya ba kasafai suke nuna soyayyar a fili ba.
Hatta a ranar masoya irin ta yau, kuma birni irin Kano mai miliyoyin Hausawa, a ziyarar da na kai wuraren da jama`a kan taru, wadanda na gani suna magagin soyayya kalilan ne.
Ganin yadda Hausawa ke dogaro ga addini wajen kaurace wa ranar Valantine, na tuntubi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, babban Malamin addinin Musulunci don ko da wani lokaci da Musulmi kan yi bikin soyayya?

Share this


0 comments:

Post a Comment

FG HAUSA | All Rights Are Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Designed By ASSALAPHY