Home

Music

Video

Kannywood
Tags:

MUGUNTA FITSARIN FA"KO 1 to 3


Subscribe Our Channel

MUGUNTA FITSARIN FA'KO📚📖

Babi na daya

Shafi na 1-3

Ban isa ofishina ba sai wajen karfe goma. Lokacin 'darin nan ne na watan disamba. Ga iska ga hazo ga kuma 'dan karen sanyi mai shiga jiki. Koda na bu'de 'kofar 'dakin kar'bar ba'ki , sai qarar kekunan rubutu kawai nakeji .mai kar'bar ba'kinmu wata banufiya ce kyakkyawa irin masu fisgar hankalin nan . Abokin aikina Faru'k ne ya tsananta aka dauke ta aiki saboda kyawun 'kirarta ba domin ta cancanta ba. Da shigata ta mi'ke ta gaisheni , ta dubi agogon hannunta sannan ta 'dage kai ta yi mini wani irin kallon baa-zata . Ni ma na san ban yi shiga mai tsari irin waCce na saba yi ba. Da ka dubi idanuna zaka san barci bai ishe ni ba. Kuma ban taba makara irin ta yau ba. Amma kuma da walaki wai goro a miya . Yau kusan kwana shida ke nan ban ga Faru'k ba; ban kuma san inda ya shiga ba. Wannan ya sa duk na fita daga cikin hayyacina, wani lokacin na kanji kamar na fada cikin 'kar'kashin jirgin 'kasa ya fi sau'ki a gareni.

    Daka na amsa gaisuwar yarinyar nan, sai ta zauna ta ci gaba da karanta irin mujallar nan ta mata. Ita dama 'dabi'arta ke nan . Kodai ka sameta tana karanta mujallun kasashen waje ko kuwa tana faman gifa jan baki. Na sha nuna wa Faru'k rashin amincewata da halin yarinyar nan. Kamfaninmu ba wajen kwalliya ba ne , kuma kamfani ne da a ka kafa bisa ga 'karfin niyya da tsananin 'kwazon matasa biyu rak, watau Faru'k da ni. Matsalar ku'din haya da albashin sauran ma'aikata da 'yan  bukatunmu na yau da kullum kadai ma sun ishe mu. In don ta nine babu lalai ga samuwar wata mai karbar baqi wadda babu abib da take yi ban da tallar kanta ga abokan ma'amalarmu . Amma ina! Gogan naka ba zai taba yarda ba. Idonsa idon kyakkaywar mace yadda ka san qudab zuma da fulawa. A kullum yakan ce "ka san duniya a ido take . Idan da irin wadannan a wuri harka ta fi tafiya daidai".

   ofishinmu 'daya da Faruq . Na bude na shiga . Ba wani babban wuri ba ne , amma ya wadace mu. Baya ga 'yan madaidaitan teburanmu guda biyu babu wani abin ku zo ku gani a 'dakin , ko da yake da n a biye ta Fauq da mun sayi irin darfumar nan mai tsada mun shinfi'da . A kowane tebur akwai irin 'yar robar nan da ake rubuta sunayen jami'ai. A wanda ke teburin Faruq an rubuta "FARUQ AWWAL MATAIMAKIN EDITAN AREWA". Daga sama a bango kusa da teburin an rataya wata kalanda mai hotunan 'yan mata tsirara. Da gani ka san Faruq dai dan duniya ne. Ngozi wata managarciyar sakatariyarmu, cewa take Faruq zai iya sanya barawo dariya a rumbu. Hakika Faruq irin mutanen nan ne da ko ba ka so, sai sun sa ka dariya. Matuqar yana wuri za ka tarar ana raha da walwala. Sau da yawa , idan na zo wurin aiki raina a 'bace FARUQ ke sa damuwa ta ragu har in kai ga murmusawa.

   Haka Allah ya yi shi kai ka ce babu abin da ke damun sa a rayuwa . In ya fara barkwancinsa da 'daidai da 'dai'dai sai kowa ya sami nashi . Shi ya sa Hausawa kan ce "kada Allah ya kawo ranar yabo " ka ga yanzu da ba faruq duk wurin kamar ana zaman makoki.

   A kan teburina akwai wasiqu da yawa da suka da'de . Na zauna na dauki guda na farke ambulann din na zaro wasiqar da ke ciki na bude . Na gan ta gwanin ban sha'awa an buga ta da keken rubutu Na fara karanta ta amma hankalina ba shi tare da ni . Rashin sanin inda Faruq ya shiga ya kshemin laka . Taradadadin halin da yake ciki nake. Amma wani lokaci sai in ce a raina , "wata kila dan duniyan nan na can yana sheke ayarsa a wani HOTEL". Amma kuma zuciyata ba ta ba ni ba. Da na dubi dimbin aikin da ke teburinsa sai takaici ya kama ni kuma zullumina ya qaru.

  A daren jiya na je manya-manyan hotel din dake garin nan wato Daba da Hamdala hotel da ma kuwa nan Faruq yake zuwa. Amma duk sun ce ba su ganshi  ba a 'yan kwanakin nan. Na kuma lelleqa irin shahararrun gidajen karuwan nan na cikin gari, nan ma ban sami wanda ya gan shi ba. Duk  da haka zuciyata tana zayyana mini Faruq kwance a gefenbwani dausayi tare da wata lafiyayyar yarinya, yana holewarsa da kwalaben giya irin masu tsadar nan . Sai dai kuma akwai wani tunanin da nake yi , ga gawar wani mutum nan lullube a cikin likkafani.......

Share this


0 comments:

Post a Comment

FG HAUSA | All Rights Are Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Designed By ASSALAPHY