Home

Music

Video

Kannywood
Tags:

KAINE SANADI 1-13


Subscribe Our Channel

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
                   AND 
Cool novel, makeup and kitchen2⃣) 

      WHATSAPP NO:
   +2347039625239
[4/11, 6:47 AM] ‪+234 703 962 5239‬: [3/6, 11:13 AM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI!*  1⃣

*WRITTEN BY*:

*FIDDAUSI SODANGI*

*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*

*EDITTED BY*
*SANAH S ISMA'IL MATAZU*

*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*

_Bismillahirrahmanirrahim_

_Godiya ga ubangijin mu Allah daya bani ikon fara rubutun nan lafiya, ina rokon Allah yasa inkare lafiya batare dawata matsala ba Ameen, wannan labarin kirkirarrene banyi shi dan cin zarafin wani ba kowata, idan yayi shige da labarin rayuwar ki ko naka ina niman afuwa hasashe ne dakuma aikin alkalami wanda yafi na takobi.

     D'akin d'aukar karatun a cike yake taf babu masaka tsinke, duk inda ka waiga babu alamar zaka iya samun wajan zama domin kuwa d'alibai ne tako ina, duka-duka k'arfe takwas ne na safiya amman kuwani d'alibi ya halarci lecture d'in kasan cewar sam mallamin babu wasa bare d'aga k'afa a tattare dashi, gashi yau d'in nan suna saka ran zaimasu test, duk kuwa da bawai ya fad'a cewa zaiyin bane, amman da dukkan alamu suna saka ran zaiyi d'in, dan shi haka yake badai yace zaiyi abu ba, saidai ya shammace ku yayi d'in. 
Hayaniyar d'aliban ne yacika d'akin karatun, wasu na hira, wasu na karatu wasu na bacci, yayinda wasu keta faman cece kuce.

  Lokaci d'aya d'akin ya d'auki shuru, tsit kakeji tamkar ba sune keta hayaniyar nan ba, masu bacci tuni sun tashi, kowa ya kama kansa yashiga taitayin sa. 

Matashin malamin ne yashigo, wanda k'amshin turaransa ya sanar wa d'aliban nasa ya iso.
 
K'yakk'yawan matashi ne wanda shekarun sa na haihuwa bazasu haura 30 ba, wankan tarwad'a ne dogo sosai ga fad'i, yanada manyan idanuwa had'e da yalwataccan gashin gira dana ido, ga wani had'add'an sajensa wanda yak'ara fitowa da k'yawun da Allah yai masa, hancin sa dogo mai k'yawun gaske.
  Sanye yake cikin k'ananan kaya, bak'in wandon Jeans ne had'e da wata jar riga mai azababben k'yau,  rigar ta d'an matse shi kad'an saita k'ara fiddo shi, k'afar sa sanye cikin wasu had'add'un takalma na maza, dagani kasan masu tsata ne,  wani dank'areran agogo ne d'aure a tsintsiyar hannun sa mai kalan bak'i sai wani shek'i yakeyi tamkar daimon. 
  

*ALIYU RASHEED GANDUJE* kenan, matashin malamin dake lokacin sa a jami'ar ta *CATHOLIC UNIVERSITY OF AMERICA*,  cikin takunsa ta k'asaita ya isa gaban d'akin karatun, inda ya k'arasa sama inda ya dace ya tsaya d'in,  tsawon minti uku ya d'auka a tsaye yana k'arewa d'aliban nasa kallo d'aya bayan d'aya, idanuwan sa suka fad'a gun zamanta inda yaga wayam batazo ba,  illa k'awar tata  mai suna,  *KHADIJA MUHAMMAD DALA* murmushi yasaki wanda ya tsaya a fatar bakin sa,  gaba d'aya d'aliban nasa sunyi mamakin ganin murmushin nasa dan sabon abu ne agare su, wannan ne yasa kowa yak'ara shiga taitayin sa, dan acewar su murmushin mugunta ne wannan *ALIYU RASHEED GANDUJE* yayi,  cikin k'warewa yashiga koyar dasu daki-daki,  gaba d'aya hankulan su nakan sa ko motsi mai k'arfi babu maiyi acikin su, tsawon minti talatin yanai masu darasin. 

K'was!! K'was!! K'was!! K'arar takalmin nata ke bada sauti, kasancewar wajan yayi shuru shiyasa k'arar ya karad'e ko ina, shi kansa *ALIYU RASHEED GANDUJE* cak ya tsaya daga bayanin sa yana kallon ikon Allah,  shidai yasan cewa babu d'alibin daya isa yashigo mashi aji bayan shi d'in yashigo, dan wannan rainin wayau ne babba acewar sa.

Hankalin ta k'wance taci gaba da takunta tana k'arasowa cikin d'akin karatun,  tafiya take cikin yanga da tak'ama,  kallo d'aya zakai mata ka tabbatar dacewar babbar yarinya ce kuma d'iyar wani babban mai mulki da sarauta, zaka gane hakan ne ta yanayin shigar ta dakuma yanayin yanda take tafiyar tamkar bazata taka k'asar ba, k'yakk'yawa ce ajin farko,  tsayawa in k'watanta maku k'yawunta k'arin bata lokaci ne gara kawai inbarku ku k'watan tota da kanku masu karatu, 
  *AMATULLAHI AHMAD FAGE*  kenan matashiyar budurwar da babu kamar ta acikin jami'ar, wajan k'yau da tak'ama dakuma nuna isar cewar ita d'in fa d'iyar shugaban k'asa ce, wohoho.....

*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[3/6, 2:36 PM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI*2⃣

*WRITTEN BY*:

*FIDDAUSI SODANGI*

*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*

*EDITTED BY:*
*SANAH S ISMA'IL MATAZU*

*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*

_Yawan comments d'inku shi zai k'ara k'arfafa min gwuiwa, insan lbrn nada masoya indage wajan yin typing dasauri_

  
        Tafiya take ko ina na jikin ta na k'adawa duk da doguwar riga ce ajikin ta amman saboda kayan datake d'auke dashi wanda Allah ya halicce ta dashi,  dole ne jikin nata ya kad'a abin gwanin ban Sha'awa,  gaba d'aya kallo yakoma kanta, itakuwa tafiyar ta take hankali k'wance tamkar ita d'aya ce a duka filin d'akin haka take ji, tana k'ok'arin zama bisa kujerar daya zame tamkar dan su aka yishi ita da k'awar tata wacce duk sanda tariga ta shigowa sai ta aje mata gu, kai koma duka basu zo dawuri ba babu mai hurumin zama a kujerar dan kuwa kowa yasan wacece *Amatullahi Ahmad Fage* da k'awar ta *Khadija Muhammad Dala*,  wani wawan tsawa yadaka mata, cikin harshan turanci yasoma magana,  "You are very stupid wacece ke dazaki shugo min aji yanzu har kike k'ok'arin zama dan bakida kunya bayan kin d'aukewa kowa hankali daga sauraron abu mai mahimman ci!" 
  "will you get out before I slap your dirty face!"

   Cak taja ta tsaya tana masa wani k'ask'antaccan kallo, kafin taja wani dogon tsaki da k'wafa tamkar harshan ta zai fita, ta doka masa wata uwar harara da manyan idanuwan ta tamkar zasu fad'o k'asa,  tafice a d'akin karatun cikin wannan tafiyar tata mai d'aukar hankali, harta bace daga cikin d'akin baibar kallon inda tabi ba, zuciyar sa tamkar ta fasa k'irjin sa tafito, lallai yazama dole yayi maganin yarinyar nan, aduk fad'in jami'ar nan ita k'adai ce ke taka shi son ranta, but lokaci yayi daya kamata yanuna mata iya karta yanuna mata ita d'in fa ba kowa bace!,  

  Hankalinsa ya maida kan abinda yakeyi, gaba d'aya ajin kowa yasha jinin jikin sa dangane da abinda yafaru yanzu,

  Awa d'aya ya bata yana koyar dasu kafin yabasu test, hankalin Khadija ne yayi bala'in tashi dan ganin k'awar tata bata nan yabada test d'in, takuma san da gangan yayi hakan saboda wannan shine test d'in shi na k'arshe yace, har nanata masu yayi duk wanda yarasa wannan test d'in to kada yasaka ran zaici jarabawar sa, nan danan idanuwan Khadija suka kad'a sukai jawur dan bacin rai,  "wai shi wannan d'an talakawan me yake tak'ama dashi ne?"  waye shi dayake taka _Amatullahi_ haka?  Gaskiya dole suyi maganin gayan nan dan isar shi tayi yawa yanaso yawuce gona da iri.

Minti ashirin kacal sukayi yasa a k'arbar masa,  ana gama had'awa ya fice abinsa,  zaune ya iske ta akan wani had'add'an Capet mai kama da jikin damisa sai d'aukar ido yake, guys d'in ta zagaye da ita kowanne ya d'od'e ido cikin bakin tabarau kallo d'aya zakai masu ka tabbatar basuda mutunci zasu iya aikata komi akan aikin su.

  Manyan idanuwan ta ta watsa akan sa tare daja masa tsaki, kallo d'aya yaimata ya d'auke kansa daga barin kallon ta, yawuce abinsa, d'aya daga cikin guy's d'in nata yayi k'ok'arin binsa saboda tsakin dayayi, ta dakatar dashi da fad'in "barshi ba Yanzu ba akwai sauran lokaci!".

   D'aliban ne suka suma fitowa daga d'akin karatun kowanne na surutu akan test d'in da _Aliyu Rasheed Ganduje_ yayi.

 Khadija ce tafito rannan nata a had'e ta zauna kusa da k'awar tata tana labar tamata abinfa Aliyu Ganduje yayi, tsaki Amatullah tayi tace "karki damu k'awata indai kud'i suna aiki a duniya zan saye Aliyu Ganduje dashi da y'an gidansu gaba d'aya,  dan haka ki barni dashi shi ai k'aramin d'an iska ne!".
  Murmushi Khadija tayi ta bata hannu suka kashe, tace har naji sanyi a zuciya ta wallahi gayen baida mutunci, hira suka ci gaba dayi abinsu cikin k'wanciyar hankali harsanda wani malamin yashiga ajin kafin suka mik'e suka shiga suma.

  Tsawon wani lokaci malamin nayi masu darasi kafin yafara watso masu tambayoyi,  tsit ajin yayi dan kuwa tambayar tad'an yimasu wuya, tsawon minti uku babu mai alamar mik'ewa, tambayar malamin yak'ara nanatawa cikin bacin rai amman tsit kake ji, ajin yad'auki shuru dayawa, can wani had'add'an gaye daga baya ya mik'e cikin turancin sa mai dad'in saurare yasoma watso amsar tambayoyin, *MUHAMMAD HUSSAIN D'ANBATTA*
kenan Yaro mai tarin baseera da hazak'a.

   Wani dogon tsaki Amatullah taja tare da fad'in banza d'an scholarship kawai!, mutum sai iyayin tsiya kowa yayi shuru amman shi yawani mik'e da banzan turancin sa saikace d'an koyo.........

*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[3/6, 5:14 PM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI*3⃣

*WRITTEN BY:*

*FIDDAUSI SODANGI*

*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*

*EDITTED BY:*
*SANAH S ISMA'IL MATAZU*

*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*

       Gaba d'aya kowa yabita da kallo dan da k'arfi tayi maganar, kuma da harshan turanci, shuru gayen yayi yana kallon ta da mamakin kalaman ta, shidai a iya sanin dayayi mata tsawon shekara biyu kenan suna tare a aji d'aya amman yasan takk'wala ce ta k'arshe, sam bata gane karatu da k'yar da sid'in goshi take wucewa kowace semester, dan haka ranshi bak'aramin baci yayi ba,  ko uban wama yace mata da scholarship yazo makarantar oho mata, lallai zaiyi maganin ta kuwa.

Sam malamin baidamu da maganar datayi ba illa iyaka yace ma _Muhammad Hussein D'anbatta_ yaci gaba da maganar sa shi suke sauraro, a k'uffule yaci gaba da koro bayani tamkar zai fashe da kuka. 

Haka sukaci gaba da d'aukar darasin har lokacin fitar shi yayi.

   ****

  Yauma course d'in _Aliyu Rasheed Ganduje_ gare su,  kamar koda yaushe d'akin karatun yacika ya batse, jiran shigowar sa kawai suke yi, Khadija ce ta dubi Amatullah tace, "yakama ta kije kiga Ganduje akan maganar test d'in ki," 
"eh yau d'in nan nake so inje daya fita zani,"
Basu k'arasa maganar ba,  k'amshin sa ya tabbatar basu cewar ya iso,  a hankali Amatullah ta furta, "barawon banza kawai!, wannan turaran dayake kuri dashi dagani kinsan satowa yayi kokuma maula yayi aka bashi!,  dan wannan turaran yafi k'arfin albashin sa wallahi!," ta k'arasa maganar cike da takai ci, k"aramar dariya Khadija tasaki wanda yasata had'a ido da Aliyu wanda ya k'araso dai-dai gefen su dan hayewa sama. 

  Basarwa yayi ya haye sama dankuwa yau d'in nan saiya wulak'anta yarinyar nan acikin d'alibai y'an uwanta tunda ita batada mutunci, yasani sarai bata san komi ba inbanda gigiwan tsiya da rawar kai, dan haka yashiga yin abinda yakawo sa ajin.

   Sanye yake cikin manyan kaya yayi bala'in yin k'yau tamkar asace a ruga, cikin k'warewa sosai yakeyi masu darasin, gaba d'aya Sun natsu suna sauraran sa.

Tsawon awa d'aya yana koyar dasu, kafin yashiga watso tambayoyi yana nuna wanda yakeso ya amsa, _Muhammad Hussein D'anbatta_ yasoma tadawa, nan ya bashi amsa ko gargada babu, dama yanasa ran hakan,  yakuma yin wata tambayar ya nuna wata d'iyar turawa, itama ta mik'e ta bashi amsa kamar yanda ya buk'ata,  daga k'arshe yayi wata tambayar ya nuna Amatullah wacce sam hankalin tama baya kansa yana kan wayar ta datake ta latse latse a ciki, Khadija nata d'an taba ta, amman ina hankalin ta yayi nisa, da k'arfi yakira sunan ta, _Amatullahi Ahmad Fage!_
  Dasauri ta d'ago manyan idanuwan ta tana kallon sa, irin kallon ne mai d'auke da harara, mamakin yanda akai yasan sunan ta take, lallai ma gayen nan d'an rainin wayau ne!, sunana dana uba na yake kira haka kamar wata sa'ar shi?  K'wafa taja dai-dai sanda yak'ara kiran sunan ta had'e da k'ara jefo mata tambayar tasa, tsaye ta mik'e kai tsaye tace "ban sani ba!,  angaya maka ni k'aramar yarinyar ce daza ka tadani gaban y'ay'an talakawa kace in amsa wata banzan tambayar ka?" 
"to wallahi Allah hawainiyar ka ta kiyayi rama ta!"
"ai dama tsiyar y'ay'an talakawa kenan, ni banma san meyasa aka d'auke ka aiki a wannan jami'ar ba, naga dai tuk turawa ne malaman amman kai bak'ikkirin k'azami dakai aka"....... Wani irin gigitaccan mari yasakar mata da hannunsa gaba da baya, sam batasan sakkowar shi ba, kawai saukar marin taji, bata gama watsakewa waba yakuma kai mata wani had'e da shak'eta yana fad'in "nine kazamin!?" hannunta yashiga ja da k'arfi yana k'ok'arin yin waje da ita sai tirjewa takeyi, a haka suka fito waje yana jaye da ita, nan danan guy's d'in ta suka yanyame shi kowanne d'auke da bindigar sa suka hayayyak'o masa tamkar zasu cinye shi..............

*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[3/7, 11:14 AM] Fdaus Sodangi: *KAINE SANADI*4⃣
         

*WRITTEN BY:*

*FIDDAUSI SODANGI*

*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*

*EDITTED BY:*
*SANAH S. ISMA'IL MATAZU*

*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*

         Fisge hannun ta tayi cikin na sa da k'arfi tana kallon yanda wajan yayi jawur, murmushin takai ci ta yi sannan ta watsa masa manyan idanuwan ta, tace _"Aliyu Rasheed Ganduje"_
Kayi k'ok'ari matuk'a! Madallah da wannan k'arfi hali naka!  Da har ka iya d'aga k'azamin hannun ka kasauke shi bisa wannan k'yak'yawan fuska tawa mai matuk'ar tsada!  To ka bud'e manyan kunnuwan ka masu kama dana zomo ka saurare ni,  wallahi wallahi wallahi Aliyu katabo ma kanka da y'an gidan ku kai da duka dangin ku bala'i da masifa, wanda wallahi nayi maka alk'awarin cewa zaman 9ja sai ya gagare ku, sai dai ku tafi can nijar dan da alama dama cirani yakawo ku 9ja dan da ganin wannan mummunar fuskar taka ansan y'an bararoji ne ku! Saboda haka ka zauna da shirin ka, "hmm! Inma banda k'addarar data hau kan ka ina kai ina taba _Amatullahi Ahmad fage!"_ 
"gaskiya ne kam d'an talaka bai iya samun waje ba, sai ya wuce gona da iri!"

Guy's d'in ta ne suka rufar masa ta d'aga masu hannu, cikin gadara da isa tace "ku k'yale shi,  ak'wai sauran lokaci bayan zuba", wani k'ask'antaccan kallo tayi masa ta tofa masa miyau tace "kasaurare ni anjima inada magana da kai!,  daga haka ta juya abin ta tai gaba, guy's  d'in nata su ka rufa mata baya,  sororo Aliyu yayi yabisu da manyan idanuwansa da su ka kad'a jawur dasu, zuciyar sa wani irin k'una yake yi, jikin sa sai k'yar ma yake dan tsananin bacin rai, lallai yarinyar nan batasan _Aliyu Rasheed Ganduje_ ba!  Kamar shi wannan k'wailar yarinyar zata wulak'an ta haka? 
Lallai watan cin uban ta ya tsaya, tunda iyayan nata basu yi mata tarbiyyar k'warai ba, "yazama dole in nuna mata ak'wai banbanci tsakanin mace da na miji!"
  K'wafa yayi ya tafi yana tad'in zuci. 

     Wasu had'add'un motoci ne kuda hud'u masu azabar k'yau bak'ak'e wuluk dasu,  kowace mota a bayan ta an rubuta  _Amatullah_ suna isa gun motocin da sauri aka bud'e mata baya, tashiga ta kame tana daddan na wayar ta, d'aya ya shiga yaja motar yayin da sauran suka raba kansu, mota d'aya ce a gaba sai wanda take ciki a baya,  sai sauran biyun suka biyo su a baya da k'arfi suka fisgi motocin suka fice daga makarantar, yau kam Amatullah ta hakura da dukkan lectures d'in, 
  Kai tsaye gidan ta suka nufa wanda ke awajan makarantar, tsakanin makarantar ma da gidan nata yakai kilomita 5, wani d'an k'aramin gida ne mai azababban k'yau,  ya tsaru iya tsaruwa, taga ita sai k'awar ta _Khadija Muhammad Dala_ ke zama a cikin gidan sai kuwa tarin y'an aiki, harabar gidan cike yake da motoci iri iri, da sauri suka bud'e mata k'ofar motar ta fito, cikin tafiyar ta ta tak'ama tashiga cikin gidan,  da sauri y'ar aikin ta mai suna Teena ta iso gaban ta tare da zubewa tana k'wasar gaisuwa, da murmushi a fuskar ta ta amsa tana fad'in "babu matsala dai ko?" 
"babu ranki ya dad'e,  meza a kawo maki?"
"bana buk'atar komi Teena, jeki abinki wanka ma zanyi yanzu,"
"to ranki ya dad'e bari inje inhad'a maki ruwan wankan,"
"ohh ohh Teena nace kibar shi kinaso kita saka ni magana" _sorry_ ranki ya dad'e, 
D'uka da harshan turanci suke maganar kasancewar Teena baturiya ce babu hausa a bakin ta. 

D'aki tashiga kai tsaye ta wuce toilet ta watsa ruwa tafito d'aure da tawul,  gaban dressing mirror ta wuce, ta yi tsaye tana k'arewa surar ta kallo,  iska ta shak'a cike da farin ciki, wani irin nishad'i takeji yanda ta gasa wa _Aliyu Ganduje_ magana cikin ruwan sanyi,  murmush tayi wanda yak'ara fitowa da k'yawun fuskar ta, a hankali ta furta "saina ga iyakar ka Aliyu Ganduje"
"ka tsokalowa kan ka tsuliyar dodo!"

  Tafi minti sha biyar gaban madubin tana ta kalailaita,  tashafa wannan ta murza wancan ta fesa wannan ta gurza wancan, ahaka dai har ta gama,  ta sanya wata had'add'iyar doguwar riga, ta fice daga d'akin kanta ko d'an k'wali babu sai wata y'ar k'aramar waya mai k'yau a hannun ta. 
Palo ta shiga ta kame a d'aya daga cikin had'addun kujerun dake cikin palon, tana lallatsa wayar, 
Teena ce tafito tace "ranki ya dad'e har kin fito?"
Kai kawai ta d'aga mata kafin tace "kije kice ma musa yatafi makaranta yajira Khadija idan ta gama ya maido ta gida"
"to ranki ya dad'e"

Da sauri Teena ta fice dan isar da sak'on uwar d'akin ta...........   

*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *KAINE SANADI*5⃣to1⃣0⃣


*WRITTEN BY*


*FIDDAUSI SODANGI*



*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*



*EDITTED BY*
*SANAH S, ISMA'IL MATAZU*



*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*



_ina matuk'ar jin dad'in yabawar ku agareni tare da k'arfafa min guiwa, nogode sosai da k'aunar ku agare ni domin duk mai son abin ka to kai yake so._

_Fatyma Izland_
_Ummi Hambali_
_Fatima Aliyu Garba_
_Zara Bukkar_
_Humaira Bashir Melody_





           Wani irin mugun kallo yake mata ko k'yaftawa baya yi, jikin sa gaba d'aya rawa yake yi idanuwansa sun kad'a sunyi jawur kamar gauta. 
A sanyaye tasaki hannun nasa tare dayin baya kad'an, matsowa yasoma yi inda take cikin wani irin taku,  zuciyar ta ce tayi wani irin bugawa nan da nan kamannin ta ya canza alamar tsoro yad'an baiyya na a fuskar ta amman cikin dakiya irin tata ta dake saidai tasoma yin baya kad'an kad'an, binta yaciga dayi har ta kurema bango, tamkar zai shige cikin jikin ta yaja ya tsaya yai mata runfa da makeken k'irjin sa.
Yafita tsawo nesa ba kusa ba da ace wani zai shigo a lokacin sam bazai yi nasarar ganin taba domin kuwa gaba d'aya _Aliyu Rasheed Ganduje_ ya lullube ta da tsawon sa dakuma fad'in sa. 
Bud'e bakinsa yayi zai mata magana wani irin had'add'an k'amshi had'e dawani irin huci mai zafin gaske yabigi fuskar ta, nan da nan y'an hanjin ta suka kad'a zuciyar ta ta yanke ta fad'i rass!! Rass!! 
Manyan idanuwan ta ta zaro tana duban sa tsoro k'arara shimfid'e a fuskar tata. 

     Cikin wani irin kakkausar murya yashi ga fad'in "meyasa kika rainani dayawa har kike tunanin zaki iya siyan _Aliyu Rasheed Ganduje?"_ 
"me kike tak'ama dashi?"
"wacece ke mekike da shi?"
"kinyi babban kuskure dakika shiga gonar _Aliyu Rasheed Ganduje_ kin tafka babban kuskure da kika shigo rayuwar Aliyu".

"Da ace zaki nimawa kanki gata dakin tattara tsummo karanki kin bar k'asar nan dan zamanki baida wani amfani, kina zaman kashe wando ne zaman dazai sa ki koma abin tausayi abin k'watance acikin makarantar nan!".

"ina jin dad'in wannan game d'in damuke bugawa nida ke! Dan haka Allah yabawa mai rabo sa'a ,kina iya ficewa daga _office_ d'ina Kafin in rufe idona in bud'e, idan kuwa ba haka ba na rantse da Allah saina illata ki anan yanzu ba anjima ba idan kuma k'aramar k'wak'walwar ki yabaki k'arya nakeyi ki tsaya in bud'e ido baki fice ba kigani."

Tsaki taja tare da fad'in "zamu had'u ne zakasha mamaki wallahi wallahi!".
  
Dasauri ta d'au jakarta tafice.

Tana fituwa suka gwabza karo ita da _Muhammad Hussein D'anbatta_ d'auke yake dawasu littafai a hannun sa, yayinda itama take rik'e da jakar ta,  littafan nashi ne suka watse a gaban ta, yayin da itama jak'ar nata ya fad'i k'asa daf da littafan. 

Gaba d'ayan su suka d'uk'a lokaci d'aya kowanne ya d'auki nasa. 
   Tana d'agowa bud'an bakin ta tace "shishigi da niman suna! To uban me kuma kazo yi a _office_ d'innan?"
"Dad'i na da d'an talaka wallahi bai iya samun waje ba!,  mutum shi ba d'an kowa ba, asalima d'an scholarship, amman sai iyayin tsiya da fi'ili."

"yanzu in banda jahilci da duhun kai irin na d'an k'auye ina kai ina bangaza ta, _Hussein D'anbatta_ kake ko uban wa?"

"To bari ingaya maka ninan daka ganni bana yafiya!, bana mantuwa!, haka nan kuma bana mance ranar d'aukar fansa!"

"Dan haka kazauna cikin shiri wannan lallausar jikin daka bangaza bazai wuce a banza ba saina nuna maka kuran ka!"

Taja wani mugun tsaki da k'wafa tamkar harshan ta zai bar bakin ta tayi gaba guy's d'in ta suka rufa mata baya.

Mamakin kalaman ta suka sa shi sakin baki yana duban ta,  lallai yarinyar nan y'ar rainin hankali ce yafad'i a fili, hmm!  Adai guji zuwa rafi.....

Khadija ce ta dube ta bayan ta zauna tace "to ya kukayi da mutumin naki?"
  Iska ta furzar cikin bacin rai tace "ai kin san komi akai da jakki sai yaci kara!"
Nayi iya k'ok'ari na amman abin ya faskara, 
Kinsan shi taurin kai gare shi da girman kai kamar shaid'an.
Dariya Khadija ta k'washe dashi harda tuntsurawa. 
"To Amatullah yanzu yaza mu bullo masa ne"
"amman kinsan me nifa wallahi guy d'in burge ni yake yi dan ya iya d'aukar wanka k'arshe wallahi."

Wani irin mugun kallo Amatullah tayi mata cikin daka tsawa tace "kar ki k'ara batan rai dan Allah!"
"meye abin burgewa ajikin wannan d'an matsiyatan?"

Kisa ido kigani muna nan za a zo a damk'i shege dan da ganin kayan daya ke sawa yana fafa dasu da turaran dayake amfani kinsan katon barawo ne!  Dan haka ina nan ina addu'a ina kaiwa Allah kuka na Allah ya kawo k'arshan sa watau watan cin uban sa ya kama a damk'i matsiyacin mai kama da k'osan rogo.

Hmm! Amatullahi kenan inaso inga ranan da wannan kiyayya taku zata k'are, koda yake shima guy d'in ne d'an rainin wayau Allah!.

**************


Bayan sati d'aya yauma kamar kullum Amatullah taki ta shirya da wuri dan sanin cewa yau lecture d'in farko ta _Aliyu Ganduje_ ce, tana ji tana gani Khadija ta shirya ta wuce abin ta, ita kuwa sai bayan minti arba'in da yafiyar ta sannan ta shirya ta Shiga makarantar ita da guy's d'in ta. 
Kai tsaye tashiga cikin ajin tana takun ta ta tak'ama, gaba d'aya k'amshin ta ya bad'e ko ina.
Cingum take tauna abin ta cike da yanga, 
Sosai ya bud'e murya yace "karki k'araso nan! Koma inda kika fito,"
Ko kalma d'aya bata furta ba asali ma ko tsakin bata yi ba yau, ta juye tayi waje tana wani jujjuya jiki. 

Cikin bacin rai yaci gaba da koyar da darasin sa. 


Kai tsaye _office_ d'in shugaban makarantar ta nufa kanta tsaye ta fad'a _office_ d'in. 
Zaune yake shida wasu manyan makarantar suna d'an tattaunawa. 
Cike da fara'a gaba d'ayan su suka mik'e suka tare ta saikace ita ce shgabar k'asar. 
Cikin fara'a shugaban makarantar yasoma fad'in "ranki ya dad'e da kanki da sassafen nan lafiya dai ko?"
Kuka ta fashe dashi sosai tana fad'in su kira Abban ta su shaida masa bazasu iya d'aukar amanar daya basu ba nata, wanda harda mak'udan kud'ad'e ya had'a masu dan dai kurum su kular masa da ita....... Da sauri shugaban makarantar ya katseta a rud'e da fad'in me akai mata?
 Cikin kuka da shasshek'a tasoma magana. 
_Aliyu Rasheed Ganduje ya tsane ni acikin makarantar nan, sam baya son ci gaba na,  baya son farincikina da k'wanciyar hankali na. 
Kullum burin shi shine yatakurawa rayuwata. 
Nashigo makaranta _last two weeks_ ya kore ni daga ajin sa, yaba da test bani,  yace duk wanda baiyi test d'in shi ba bazai ci jarabawar saba. 
Nabishi _office_ d'in sa nabashi hakuri yace sai dai in siya test d'in da kud'i,  na bashi kud'i masu yawa yace shikenan magana ta k'are. 
_last week_ yakira ni _office_ d'in sa bayan naje yake cemin shi ya janye zancan kud'i saidai inbashi kaina,  tak'ara fashewa da kuka mai cin rai duk wanda yagan ta a lokacin sai ya tausaya mata."

"ina son karatuna sosai saboda burin mahaifinane insamu ilimi sosai kuma kun sani, wannan dalili yasa nabawa _Aliyu Rasheed Ganduje kai na saboda kawai yadai bani test d'in nan kada infad'i jarabawar sa."

"A bin mamaki yau ya tare ni dazancan saidai in k'ara bashi kaina saboda test d'in nan ba abu bane mai sauk'i dazai iya bani shi haka a bagas."

"na nuna masa sam ban yarda ba tunda abin nasa rainin hankali ne shine wai dan nashiga lecture d'in shi yanzu ya koreni daga ajin, tak'ara fashewa da wani irin kuka tamkar zata shid'e........... 




*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *KAINE SANADI* 1⃣0⃣to1⃣5⃣



*WRITTEN BY:*

*FIDDAUSI SODANGI*


*STORY BY:*
*KHALISAT HAYDAR*


*EDITTED BY:*
*SANAH S, ISMA'IL MATAZU*



*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*



_wannan page d'in nakune_

_Anty Sadiya Jegal_
_Safreenah Annour_
_Abeeda_




           A fusace shugaban makarantar yace _"what!_ dama duk cikin turan ci suke maganar, yaci gaba da fad'in _Aliyu Rasheed Ganduje_ ne ya aikata wannan mummunar..... D'aya daga cikin wa'yan da yake tare dasu ne ya katse shi da fad'in karkayi mamaki zai aikata fiye da hakan!  Ai d'an iskan yarone ak'wai yarinyar data taba kawo min k'arar sa nida kaina naja masa kunni aka rufe maganar to kaga yanzu yakuma maimaitawa inda bazamu taba k'yale shiba!,  _(kai jama'a kuji k'arya k'iri-k'iri)_

Cikin muryar kuka tace "idan ma baku yarda da zance naba muje ajin a tambaye su, domin kuwa su shaida ne, suna kallo ya kore ni rannan yayi test, yau ma suna kallo yakore ni, har marina yayi rannan duk agaban kowa akayi nasan zasu fad'i gaskiya, sannan kuma _Muhammad Hussein D'anbatta_ shaida nane, domin kuwa yaga fito wata daga _office_ d'in _Aliyu Rasheed Ganduje_ ranan dana kai masa kud'i. 

A fusace shugabar makarantar ya tasata gaba ita da sauran malaman suka nufi _department_ d'in nasu, kai tsaye ajin suka nufa ,
Yana ta koyar wa abin shi cikin k'wanciyar hankali da k'warewa. 
Koda ya hango su baisa ya tsaya daga abinda yake ba illama k'ara sautin shi dayayi wajan baya nin daya keyi. 

Saida suka k'araso har gaban ajin sannan Aliyu yayi shuru yana duban su.
  Shugaban makarantar ne yafara magana a fusace bayan ya fuskan ci y'an ajin, "yau shene kukayi test d'in _Aliyu Ganduje?"_ yayi tambayar cikin dakakkiyar murya da harshan turanci. 
Gaba d'aya suka had'a baki suka sanar dashi.
Kai ya gwad'a kafin yace  "kunsan wanna?" yanuna Amatullah, suka bashi amsa dacewa nan ajin take, yace "a ranan da Aliyu yayi test d'in sa ya kori Amatullah kokuwa?"
Suka sake bashi amsa da tabbas anyi haka, yakore ta sannan daga baya yarubuta masu test. 
Yasake cewa "yau tashigo ajin nan kobata shigo ba?"
Suka sake bashi amsa dacewa tashigo yakore ta saboda dama shi k'a'idar sa indai yariga ka shigowa to koran ka zaiyi.
_"where is Muhammad Hussein D'anbatta?"_
Mik'ewa yayi tare da fad'in _"am here sir!"_

"inaso in tambaye ka tsakanin ka da Allah zaka gaya min, idan ka boye min kokari min k'arya baza ka boyewa Allah ba saboda yana kallon ka!".

Kai _Muhammad Hussein D'anbatta_ ya d'aga masa alamar zai fad'i gaskiya. 
  "kataba ganin wannan y'ar ajin taku tafito daga _office_ d'in _Aliyu Ganduje_ ko za ta shiga?"

Shuru Muhammad yayi tsawon wani lokaci shidai bai san make faruwa ba amman tabbas dai yasan ya taba ganin ta tafito harma ta gaggaya masa bak'ak'en maganganu, wanda har gobe sunai masa ciwo matuk'a. 
  Dan haka yace "k'warai kuwa idan ban manta ba anyi sati d'aya kenan dana ganta tafito daga _office_ d'in _Aliyu Ganduje_ 
_"good"_ 
Shugaban makarantar ya furta da k'arfi, sannan ya dubi Aliyu wanda yayi sororo yana kallon sa, zuciyar sa yana tafasa meyake shirin gani haka yau?
Kamar shi shi _Aliyu Rasheed Ganduje_ za a wulak'anta a cikin yara k'anana!  Way'anda suke ganin girman sa da mutuncin sa!?
Lallai yarinyar nan ta d'auko ruwan dafa kanta yau!

Wani mugun kallo shugaban makarantar yayi masa kafin yafara magana cikin masifa, "dama nasan cewa baza ta yi maka k'arya ba, domin d'an babban gida baya k'arya!,  kawai nazo ne dan in fita hakkin ka ayi komi a gaban ka kana gani dan kar kace anyima sharri ko k'azafi!. 
Ya kalli Amatullahi yace "ranki ya dad'e maimata abinda ya had'aku agaban sa yaji dan yasan komi ya iso kunnin mu, kuma dama yasan dokar makarantar nan dan haka sai ya yankewa kansa hukunci da kansa. 

Babu kunya babu tsoron Allah Amatullah ta maimaita abinda tace masu babu ragi babu k'ari. 
Shugaban makarantar ya dubi Aliyu yace "meza ka iya cewa akan abinda ta fad'a?"
Bud'an bakin Aliyu sai cewa yayi gaskiya ta fad'a anyi haka. 
"murmush Amatullah tayi tace ai bai isa ya k'aryata ba tunda yasan cewa tabbas ya aikata.
  Wani irin kallo Aliyu yake mata cikin ido mai wuyar fassarawa, gira ta d'aga masa ta kashe masa ido d'aya. 

"to Aliyu Ganduje kana iya zuwa _office_ d'ina domin ka amshi takardar sallama, domin kaima kasani wannan shine hukun cin duk wanda aka kama da irin laifin ka. 
Daga haka suka fice gaba d'ayan su har Amatullah tabi su tana karkad'a mazaunai. 

Kaf miyan bakin Aliyu ya kafi da k'yar ya iya tattaro numfashin sa gu d'aya har ya saisai ta kansa. 
Idanuwan sa sam babu k'yawun gani. 
Cikin wani irin tafiya mai kama dana bijimin sa yafice daga cikin ajin. 
Gaba d'aya d'aliban jikin su yayi sanyi da ace sun san wannan ne dalilin da yasa akai masu tambayoyi ai da basu fad'i komi ba sun rufa masa asiri domin kuwa koba komi suna gane lectures d'in sa. 

Khadija kuwa hawaye ne taji yana gudu bisa fuskar ta wanda ita kan ta batasan dalilin saukar suba. 

*******


Bayan awa biyar, Amatullah ce ta k'ure k'arar radio tana shan sauti tana tik'ar rawa daga ita sai wata yar _vest_ da guntun wando. 
Rawa take hankalin ta k'wance dagani kasan tana cikin nishad'i,  wani irin rawa take tamkar zata karye, sai kace wata bebin roba. 

Khadija ce tayi sallama tashigo amman sam Amatullah bata san da shigowar taba. 
   Khadija tafi minti biyar da shigowa amman sam Amatullah tayi nisa a sharholiyar ta. 
Wani irin juyi tayi cikin rawar ta kawai sukai ido hud'u da aminiyar ta Khadija.
Dasauri ta kashe radio d'in cikin ihun murna ta rungume Khadija tana fad'in _i am the winner of the game_ sis kitayani murna, nagama da _Aliyu Rasheed Ganduje_ nagama dashi wallahi.

"Yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa,  Allah nagode maka daka bani sa'a akan mak'iyina."
  "Khadija na dad'e banyi farinciki irin na yau ba wallahi,"
Na maida Aliyu abin kwatan ce a duniya,  
"yace wai in tattara tsummokarana in koma k'asata."
"to gashi nan kafin ni in koma matsiyacin ya riga ni."
"hmm!! Ai duk wanda yaci tuwo dani wallahi Allah miya yasha!"
"in banda _Aliyu Rasheed Ganduje_ ina shi ina ja da d'iyar manya!"

"ai bigi sai big! Babban goro sai magogin k'arfe!"
"Hmm!!  _Aliyu Rasheed Ganduje_ *KAINE SANADI*
amman sam bahaka Amatullah take ba, kaine ka canza ni nazama haka.

Sai a lokacin ta lura da yanda Aminiyar tata ta tsaya mata cak tamkar wata gunki bata taya ta farin ciki. 
Jiki a sanyaye ta sake ta tanai mata kallon tuhuma. 
"Khadija lafiyar ki kuwa?"
Cikin muryar kuka Khadija tasoma magana, "Amatullah sam banji dad'in abinda kikai ma Aliyu ba!  Sam baki k'yauta ba."
"ina so ki sani Allah ya jarabceni da k'aunar _Aliyu Rasheed Ganduje_ tun daga ranan dana soma ganin sa!"
"ina son Aliyu ina k'aunar sa ina kuma burin in mallake sa,  sai gashi cikin k'ank'anin lokaci kin rusa min lissafi na!  Amatullah  bakiyi min adalci ba kin ma rayuwata illa babba!, yanzu ta ina zani niman Aliyu ina zanbi ingan sa, dawani ido zan dube sa?" tafashe dawani irin kuka mai taba zuciyar mai saurare.

Wani irin kallo Amatullah keyi mata ko k'yaftawa batayi, kafin tafara magana cikin rashin mutunci mai cike da masifa. 
"Khadija ashe bakida mutunci bansani ba! Ashe zaune nake da makiyiya ta bansani ba?"
"haba! Tabbas biri yayi kama da mutum."
"lallai d'an adam butulu ne"
"to bud'e kunnuwan ki kiji ni da k'yau!  Daga yau sai yau,  bani baki!  Ke ko a hanya kika ganni kika nuna kinsan ni Allah ya isa ban yafe maki ba!  Kuma ki tattara kayan ki kibar min gida na yan zunnan bada bata lokaci ba"
"banza mara zuciya!  Inbanda Kare ya cinye zuciyar ki ina ke ina Aliyu Ganduje?"
"mutumin daya tsane mu nida ke baya k'aunar ya bud'e ido yagan mu a duniya!  Wai shi kike k'auna!  To ki k'arawa motar ki mai kibi Aliyu Ganduje gidan matsiyacin uban sa yayi maki wajan k'wana acan."

Taja tsaki tanimi kujera ta kame tana ci gaba da masifa......... 

Share this


0 comments:

Post a Comment

FG HAUSA | All Rights Are Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Designed By ASSALAPHY