Home

Music

Video

Kannywood
Tags:

SUMAYYA 1-10


Subscribe Our Channel

    Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239
   💝💝              
         💝    *sumayya*    017

     _an amazing lovestory_
________________________
by *ayshalove* 😍


      🎀  *dedicated to 5 alive family* 🎀


*GARGADI*
wannan lbrn qirqirarrene banyishi don cin mutunci wani ba ko musgunawa wani nayishi ne don masoya krtun littafi su nishadantu kuma su fadakantu
*pls dont edit*
duk wanda y canja min wani abu allah ya isa ban yafeba


first nd second pages

yarinyar yar kimanin shekara 20 ce a gaban dressing mirror, fara ce mai launin madara tanada ido masu matuqar jan hankali, lips din ta cute ne launin pink ,hancinta dogo ne amma ba mai tsayi ne sosai ba dan karami
face dinta yar madaidaiciya, gashin kanta baqi ne mai kyalli musamman daya sha mai, ba gajeriya bace kuma ba zabgegiya bace yar madaidaiciya,


atampha ce ajikinta purple nd black dinkin riga da zani rapper, wanda ya xauna a jikinta kamar siket


ta gama kwalliya dan kunne take sakawa , sannan tasa awarwaro wanda ya qarawa hannunta kyau sbd xanen lallen dake hannunta kasancewarta ma'abociyar son baqin lalle

bata saka sarqa ba powder ta dan shapa sannan tasa kwalli wanda ya karawa idon ta haske, tasaka lip glow ta dau mayafi ruwan kayanta dama tayi daurin dankwali sannan ta shafe jikinta da turare....
tsaf ta fito
           *sumayya kenan*
 wata matace xaune a kan daya daga cikin kujerun da suke falon ba wani kudi a ka kashewa falon ba da gani kasan mahaifiyar sumayya ce sbd kalar fatarta tayo

kusa da ita kuma yrnya ce 'yar kimanin shekara 17 wacce kamarsu daya sak da sumayya banbancinsu kawai launin fatane kasancewar ita dayar chocolate colour ce sai  wani dan tabo dake fuskar sumayya can kasan girarta kalar baki wanda  qaramar bata dashi
sannan kuma ita qaramar nada dimples wanda sumayya bata dashi

tsugunnawa tayi kusa da matar tare da fadin
"ummiy na fito xamu tafi"
ummiy tace
"to sumayya Allah y kiyaye ki kula kar kuyi dare kinji"
ta amsa da to ummiy insha Allah

yarinyar dake kusa da ummiy ce tace
"sis sumy a dawo lpia"
ta amsa da
"Allah y sa little sis zee


wani saurayi ne xaune acikin mota acikin driven din gidan baki ne amma kuma black beauty ne yasha qananan kaya masu matuqar kyau da tsada
        *yusuf kenan*


 kallonta yake ta famanyi tun fitowarta har  ta kwan-kwasa glass din motar sannan ya farfado daga dogon tunanin da ya tafi. tasa hannu ta bude kofar ta shiga motar ta xauna wani irin shegen kallo yake mata a kunne ya rada mata me yasa kka bude motar bayan kinsan banso ki wahala kinga yadda kika yi kyau ga wani kamshi da yake tashi a jikinki? ta dan kau da kanta gefe ya yusuf mu tafi kar muyi dare. tanada kunya sosai tana jin dadi yadda ya yusuf ke bata kulawa. murmushi yayi ya tada mota suka tafi.

pg «03» & «04»


tare suka fito daga shop din  bayan sun gama siyayyar da sukaje yi ta kayan kwalliya da ya takura sai ta yarda sun je. a dan tsorace ta kalli hannunta
" ya yusuf kaga wayata?
" a,a my d"...
" oh no inaga na barta a stairs din bene bari naje nai maxa na duba".
 shan gabanta yayi da sauri
" ya xa,ayi na barki kije ni bari naje",,,
"a'a ya yusuf karka damu ka saka kayan a mota nima yanxu xan dawo kuma kaga ai xanfi sanin inda xan duba"...
"ok since u insist my d ur wish ix my command"

tayi sa,a taga wayar a inda take tunanin ta mantata......

" aaaasssh ta fada tareda ambaton Allah yayin da taji kanta ya bugu da nashi ta dago da sauri wani saurayi ta gani yayi mata kalar sani.....
" *am sorry* "
 duk suka hada baki...
 " *ix okey* "
 nan ma suka kuma hada baki sukayi wajen fada...duka sukayi murmushi  sannan kowanne yayi hanyarshi.
 wajen 5:30 ya yusuf da sumy suka dawo gida.
ta dakko kayan da ta suyo ta bawa xynab nata ta bawa suhail chocolate din data siyo masa.

"laaaa sister wlh namanta na fada miki sis rayher taxo tace na fada miki in kin dawo ki kirata"
 zainab ce ke fadawa sissumayya,,,,
"ohh kuma sai yanxu kike fada min ko zeey...
"ai nace miki mantawa nayi sister,,
"ok shikkenan


"friend ,
"ni karki kirani frnd, yau na ajiye frndship din tunda baki damu daniba..saboda Allah sai yanxu kka gadamar kirana
"kiyi hkr my only best frnd, my sis,my love  am sorry once again... ba laifina bane zynab ce ta manta bata fadamin ba sai daxu ana magrib
"to amma yanxu inace karfe 8:30...
" eh nayi tilawane kuma nayi sallar isha,,,
"shikkenan gobe a mkrnta mayi mgn, akwai lbri ne? sosai ma kawata to allah yasa muji alkhairi ameen rayher ta amsa olryt bye, suka kashe wayar....

pg «05» & «06»


kashe wayr ke da wuya
sai taji ihu  a tsakar gida a ranta tace oh ni sumayya mutum kullum aiyi ta dukanshi kamar jaki amma baya hankali..da sauri ta fita ta rike bulalar da yake ta xabga mata
"kawu don Allah kayi hkr, baxata sake ba",
 a tsugunne take a gabanshi, ta juya kan wadda ake duka
" haba khadija kullum ke sai an dukeki dan Allah kiyi hnkli"
wanda sumayya ta kira da suna kawu yace
" barni da ita jikin ta ya gaya mata"
duk mutanan gidan sun fito waje ba wanda ke iya sa baki idan kawu nuru yana fada ko duka sai sumayya... zulaiha matarshi wato babar khadija wacce suke kira da mama tace "wai me tayi makane haka kke ta dukarmin 'ya,,,,
"ke kuma munafuka harda kara xugashi ko?? ta dunguri kan sumayya",,
" a,a wlh mam....
" yi min shiruuu ta daka mata tsawa.
ummi ce taxo taja hannun yar tata don tasan halin zaliha batason sumayya, daidai lkcn da baban sumayya (wanda suke cewa abiy) ya shigo.
"ummi ina xaki kai sumayya?
 abi ne ke tmbyar ummi.. zainab ce ta fada mai duk abinda ke faruwa... yace
" haba nuru meye haka shifa duka ba abinda xai kara sai lalacewa addu'a ita ce komai..... kawu nuru ne yace
"yaya wlh yarinyar nan ta ishe ni,,...
" to ni bata isheni ba"
 mama ta fada cikin tsiwa
 ai kuwa kawu yayi kanta abi ne ya rike shi
"kiyi mana shiru"
cewar abiy
 ai kuwa taja hannun khadija sukayi bangarensu.... abi ya kalli kawu
" hkri xakayi.. wai me tayi makane?
" hmm kama yarinyar nan nayi tana sata a dakin inna,, shi ne nace suhailu ya fita makota da inna in yaso sai in xaneta inna bata nan balle ta hanani"...

rayuwar gidan su sumayya kenan ko da yaushe akwai sabon abinda ke bullowa



kiran sallar asuba ne ya tada sumayya wacce dama ta saba tashi duk asuba,, tayi addu,a ta wanke baki tayo alwala.. kafin a tada sallah a masallaci ta wuce kicin ta share ta goge ta dora ruwan wanka tun da yau monday kowa xai fita sannan ta dora ruwan tea.. ta dawo daki ta tada sallah... bayan ta idar tayi azkar... lkcnne ummi ta tashi tayi sallah kafin ummi ta idar da sallah har tayi wa suhail wanka ta tashi xynab tayi wanka ummi ta shiga kitchen don hada kayan kari don sumayya na qaunar wanka sai tayi kusan awa daya a bandaki tana wanka a hakama in tana sauri kenan... basu jima ba suka kammala komai suka wuce mkrnta...

*wacece sumayya?*


pg «07» & «08»

           
wacece sumayya?

sumayya yarinya ce yar shekara ashirin(20) wacce take da kannai biyu zainab da suhail,
zainab shekararta 17 wacce take lvl 1 ita kuma sumayya take level 3 a bayero university take karantar physiology,,
suhail yaro ne dan shekara 9

kakansu sumayya (mlm shehu)  yanada 'ya'ya  uku zaharaddeen ne babba sai kamaluddeen sannan nuruddeen.

zaharaddeen yanada da guda daya wato yusuf,,, kamaluddeen shine mahaifinsu sumayya,,, yayinda nuruddeen(wato mahaifinsu khadija) yake da 'ya'ya 5

khadija, umar, aisha, hafsat, teemah.


mlm shehu mutum ne na mutane yanada tarin ilimi Allah y bashi, yanada gonakai don 'ya'yanshi ma duk sunada ilimi amma duk da haka kamaluddeen(wato mahaifinsu sumayya) shi ne yafi maida hankali sosai don shi yafi son karatun don har saudiya yaje karatu sbd mlm shehu yanada dukiya da gonakai da shanu,

 yayinda babban danshi zahraddeen ya fi karkata akan kasuwanci. yake aiki a wani company na robobi  inda ya tara dukiya daidai gwargwado yake kuma taimakawa yanuwanshi. shikuma nuruddeen yafi maida hankaline wajen noma da kiwo inda shima yake samu don duk cikinsu ya danfisu samu

kafin mlm shehu ya rasu ya bar wasiyya ko ba ranshi ayi auren sumayya da yusuf don kara karfafa xumuncinsu. sbd duk cikin jikokinshi yafison sumayya sbd yarinyace mai hankali

gidan su sumayya babbane (family house) yanada part hudu kowanne a wadace.  dukkansu tare suke xaune kowanne da matarsa. daga baya da Allah y horewa babansu yusuf sai farida matarshi ta takura mai sai ya gina masu nasu gdn sun tashi a cewarta ana samasu ido,, kasancewar shi mutum ne mai jajircewa yaki yarda yace shi tare da 'yanuwanshi xai xauna,,
da Allah y kara hore mishi sai suka hadu shida kawu nuru suka sake qawata gidan sukayi mai fenti suka fitar da garage sai suka sayi family car guda biyu

 tun daga nan zaliha da farida suka hade kai suna musgunawa amina(mahaifiyar sumayya).  

mlm shehu dan asalin garin kano ne, ya auro matarshi shamsiyya (inna) daga adamawa da yaje kasuwanci daga nan ya tsaya neman ilimi har Allah ya hadasu sukayi aure ya dakko ta ya dawo da ita garin kano suka cigaba da rayuwa inda suke xuwa ganin gida lkci xuwa lkci,,,

sumayya da rayher qawayene da suka taso tare kasancewarsu maqobta tare sukayi primary,secondary har xuwa jami'a
jamila qawarsuce wacce suka hadu da ita tun lvl 1 dinsu saidai ita iyayenta masu haline

sumayya tanada kyau matuqa shi ne dalilin dayasa yusuf yakeson aurenta


pg «09» & «10»



"gsky yau lectures dinnan ba tayimin dadi ba(so boring)"..
sumayya ta kalleta da mamaki

" haba ryhanat ai kuwa mlmin nan ya iya koyarwa kece fa kike yabanshi akan koyarwa kodai kina tunanin wani abu ne?,,, oh na gane kice kina tunani jamcy ne,, Allah sarki jamila wlhy ina missing dinta,
 rayher ta dafa ta nima haka wlh
sumayya tace
 "shi yasa bakiji dadin lectures din ba?..
rayher tayi ajiyar xuciya tare da fadin
"hmmm kedai bari ai wlh na qagu mlminnan ya fita in baki lbrin nan"...
sumayya tace
"to bani nasha qawata"
rayher tace
"shekarnjiya a bikin jamila  kinsan ta auri abokin M.k....

"eh inajinki",,, sumayya ke fadin haka..
rayhanert tace
" to zaki iya tuna kanin M.k?
 "to aini ko M.k ma baxan tuna ba gsky "
inji sumayya
rayher ta dora
"to dai yanxu kanin M.k wato khabir(k.b) shi ne yace yana sona ta karasa maganar cikin ihun murna"...
sumayyace ta dan bugeta.
" ke da allah ni kin dame ni ya isa haka"..
"amma ni bansan wannan kanin M.k dinba"..
rayher tace
"eh ba lallai ki sanshi ba sbd kafin yaxo kun tafi..
" ok"
 sumayya ta fada.. rayhanert tace,
" amma ai xaki iya sanin M.k ki tuna wanda ya xauna kusa da ango wani mai hanci wanda har na taboki nake nuna miki shi.... ohhh na ganoshi.. can sai sumayya ta tuno da wanda sukayi karo a shop dinnan ai M.k ne.........

rayherna ta dafa kafadar ta tare da fadin

"tunanin me kike haka ko har yanxu tunanin tuno M.k dinne

sumayya tai murmushi
"ina tuna mun taba haduwa da shi ne a wani shop kuma yana da mutunci don baxakice mai kudi bane... qaran wayar rayherna ne ya katse su daga hirar da suke wacce sumayya tayi matuqar jin dadinta
" hlo....... ok durling ga munan
ta taba sumayya
"tashi muje k.b yaxo kuma inaso na hadaku
"ok muje ,,sumayya ta fadi

sallama sukayi yayin da suka isa daidai in da yake tsaye jikin wata mota firgigit y dawo daga tunanin da yake,, wanda tunda suka taho ya tsura musu ido baxaka gane wa yake kallo ba a tsakaninsu(sumayya ko rayher) sumayyace tai magana
" lallai angon naki ya tafi tunani irin wannan kallo haka ta matsa kusa da ita daidai kunnenta irin wannan so haka..

Share this


0 comments:

Post a Comment

FG HAUSA | All Rights Are Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Designed By ASSALAPHY