Munari Niger: *KA HA'INCE NI😭*
*A TRUE LIFE STORY*
*BY*
*ANTY MAIMOUNATH O.G*
*💦TALENTED WRITERS FORUM💦*
*T.W.F*
*Had'in kan mû abin alfaharin mû🤝k'ungiya d'aya tamkar da dubu*
*_ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN,NA SAKE DAWOWA CIKIN WANI SABON NOVEL DIN KUMA,YA ALLAH DA AMINCEWARKA ZAN FARA,KA YARJE MIN IN GAMASHI LAFIYA_*
*_FAN'S ZAKU GA BA NOVEL DIN DA NASO YI BANE,HAKAN YA FARU NE A DALILIN WANNAN LABARI DA ZAN KAWO MUKU,DON ISAR DA WANI SAQO GA AL'UMMA_*
*_IDAN NAGA ZAN IYA HADA BIYU KUWA TO ZANYI MUKU TYPING HAR DA IRFAAN INSHA ALLAH,AMMA BANYI ALK'AWARI BA,INA GODIYA DA BIBIYATA DA KUKEYI,MUJE ZUWA_*
*_GARGAD'I_*
*_BAN YADDA WANI/WATA SUYI AMFANI DA WANI SHAFI NA WANNAN NOVEL DIN BA,TRUE LIFE STORY NE,PLX A KIYAYE👏🏻*
*_DEDICATED TO_*
*_ANTY HASSANA ATK_😘*
*1-5*
Gida ne d'an madaidaici,da gani masu gidan ba masu akwai bane saidai rufin asirin ubangiji,
Wata 'yan mata ce 'yar k'imanin 17 yrs ta fito daga gidan sanye da uniform na makaranta duk sun kod'e alamar sun tsufa Kenan amma dai a wanke suke tas,
A hankali take tafiya da ganinta kasan da abinda ke damunta,wata yarinya ce ke ta kiranta a baya bata ji ba har saï da yarinyar ta jimmata tare da dafata,
''Wlhy Sadiya har kin bani tsoro'',
''Kajiki to ai kece inata faman kiranki amma kin kyaleni tunanin me kikeyi ne haka?",
Ta nisa tace''hmm Sadiya Kenan kawai ina tunanin rayuwa ne'',
''Haba HAMIDAH tunanin rayuwa kuma kina 'yar k'aramar ki haka kawai kisa ma kanki damuwa har wani ciwon yazo ya kamaki?",
''Hmm Sadiya bazaki gane bane,ina cikin *k'uncin rayuwa*,ki duba ki gani da yanda muke rayuwar babu,kinsan komai ai ba sai na fad'a miki ba'',
''Duk da haka *HAMIDAH* ki rink'a sawa kanki salama shifa komai na rayuwa mai wucewa ne,innallaha ma'as sabirin,dukkan tsanani yana tare da sauk'i'',
''Allah yasa mû dace,muyi Sauri kinsan halin malam da mutum yayi late zai yi mana hukunci'',
''Ameen k'awata, to muje gaskiya kam'',
><><><><><><><><><><
*Wacece HAMIDAH?*
*HAMIDAH* 'ya ce ga malam Abdu da Umma Zuwaira,suna kiranta da umma kawai,asalin su 'yan Kaduna ne,Suna zaune ne a unguwar Rimi,HAMIDAH su hud'u ne wajen iyayen su,tanada yaya guda da kuma k'anne biyu,
D'an fari shine Mujaheed,sai ita *HAMIDAH*,Shafa'atu,sai autan su Ahmad,
*HAMIDAH* tanada kyau na nunawa sa'a,ga diri,Abu d'aya ne kawai dan Allah bai yisu masu arziki ba,kayan sawar ma dai maneji akeyi,
Kyawun ta da d'aukar hankalin ta yasa kafin suyi candy samari sukayi mata caa,ita kuma bata k'aunar ta bud'e ido taga wani d'a namiji a gabanta saboda ita a ganinta wahalalliyar rayuwar da suke ciki ma ta isheta,
A haka yayan k'awar ta Sadiya yace yana son ta,amma bata amsa mishi ba,sai kwawarshi yakeyi,ita dai bata son tayi mishi wulak'anci ne saboda k'awarta,
Sun taso cikin rashin wadata sakamon ba wani aiki mahaifinsu yake ba,sai dai 'yan bige bige kawai,idan anci na safe ana tunanin abinda za'aci da rana ga kuma na dare,abin dai ba'a cewa komai sai alhmdllh,wannan Kenan.......
*Cigaban labarin....*
Yau da wuri suka taso, suna kawowa daidai inda zasu rabu sai ga Jamil yayan Sadiya yanaso yayi ma *HAMIDAH* magana amma ganin suna tare da Sadiya yasa yasha mur gaishe shi sukayi kowacce tayi gidansu,
Ta iske umma tana tankad'en garin tuwo a tsakar gida taje kusa da ita ta zauna,
''Umma aiki ne kikeyi kawo in tayaki,ina ita shafa'atu take yau ko makaranta bataje ba?",
''Ki barshi ke da yanxu kikazo,kije ki cire kayan naki tukun,Shafa tana cikin d'aki a kwance wai kanta ke ciwo'',
''Subhanallahi d'azu fa lafiya lau na barta har tana cewa itama gâta nan xuwa makarantar'',
''To kinsan jiki da jini ita cuta ai zuwa take kawai ba tare da tayi shawara ba,haka mutuwa ma'',
''To umma bari in shiga in ganta'',
Tashi tayi ta nufi cikin d'akinsu......
Bayan kwana biyu da misalin 5 na yamma *HAMIDAH* tana zaune a tsakar gidansu tana lesson sai wani yaro yayi sallama yace ana Kiran *HAMIDAH*,
''Je kace bata nan'',umman su da ke fitowa daga d'aki tace''kai kace tana zuwa'',yaron yace''to'',yayi waje da gudu,
K'arasowa tayi wajen da HAMIDAH ke zaune tace''wai ke me ya ke damunki ne,ba kiranki akeyi ba da zakice ace bakinan?",
''Nifa umma bason fitar nan nakeyi ba,kuma ma ni bansan ko waye ba'',
''Duk da haka dai kije kigani ko waye da kuma dalilin xuwan shi'',
Ba dan taso ba ta saka hijabinta tayi waje,tana fita bakin soron gidansu,wa zata gani,JAMIL ne yayan k'awarta Sadiya,tayi mamaki sosai har sai da ya gane hakan,
Gaishe shi tayi kanta a k'asa,yace''hmm *HAMIDAH* kina mamakin kwawa irin tawa ko?kema dai kinsan bazan iya hak'ura dake ba dan haka kawai ki kar6i soyayya ta ni aurenki nakeso inyi'',
''Dan Allah yaya JAMIL kayi hak'uri ni karatuna zanyi babu zancen aure ko soyayya a gabana'',
''Hmm zan dai k'ara miki lokaci kiyi nazari da kyau'',yana gama fad'ar haka ya ficewarshi.....
*Comments naku shine k'arfin gwiwata*
*'Yar mutan kazay ce👉👑*
*Anty Maimounath O.G*
[20/04, 18:42] Munari Niger: *KA HA'INCE NI😭*
*A TRUE LIFE STORY*
*BY*
*ANTY MAIMOUNATH O.G*
*_💦TALENTED WRITERS FORUM💦_*
*T.W.F*
*Had'in kan mû abin alfaharin mû🤝k'ungiya d'aya tamkar da dubu*
*_🤔NI KAM INA MAMAKIN MASU BINA PRVT SUNA CEWA IN TURA MUSU PIX DINA SUNA SON SU GANNI,NOVELS KAWAI NAKE RUBUTAWA BAN RABA PIX,PLX KU DAINA,DA MASU YIMIN VIDÉO CALL,KUMA KU DAINA BAZAN DAUKA BA,BA WULAK'ANCI BANE KO GIRMAN KAI,PLX KU FAHIMCENI👏🏻_*
*_DEDICATED TO_*
*_ANTY HASSANA ATK😘_*
*6-10*
Nan ya barta tsaye baki bud'e ita mamakin shi ma takeyi, wai ma ana soyayya Dole ne,oho,shigewa tayi cikin gida fuska ba walwala,
Ko da umman su ta ganta ma bata tambayeta komai ma ta shige d'aki kawai,
A haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya gidansu *HAMIDAH* suna cikin wahalar abinci wata rana sai a wuni ba'a dora girki ba,sai abban su yayi 'yan bige bigen shi zai samo a dafa na dare shima da k'yar abin dai ba'a cewa komai,
Haka ta dage domin tayi karatu ko dan ta samu ta zama wani Abu a rayuwa tunda yayan nasu ma ba karatun ya gama ba bare ya taimaka da wani abin,karatunshi ya tsaya ne saboda rashi da suke fama dashi,
Bayan wasu watanni sai ga kanwar umman su tazo daga bauchi dan tafiya da *HAMIDAH* tace zata kaita can tayi karatun kuma dawainiyar zatayi ma umman su *HAMIDAH* sauk'i,
Da JAMIL yaji wannan labarin ai kuwa hankalin shi ya tashi domin a ganin shi ya fara samun kan *HAMIDAH* amma gashi zatayi mishi nisa,tunda yanxu tana saurarenshi sunayin hira kad'an kad'an,
Washe garin zasu tafi bayan isha'i yazo gidansu,duk jiki a sanyaye bayan sunyi hira ne ya mik'a mata waya da sim da komai a ciki da k'yar ta amsa yace zai rink'a kiranta da wayar,
Nan dai suka rabu tayi shigewarta gida,amma bata bari kowa yaga wayar ba saboda kar umman su ta gani tayi mata fad'a,hmm
******************
Da misalin k'arfe 10:30am suka bar garin Kaduna,a mota *HAMIDAH* sai kukan rabuwa da iyayenta takeyi tana tunanin *rayuwar k'uncin* da suke ciki,lol
Sai da kanwar umman su ta rarrasheta sannan tayi shiru,tana ta kallon hanya wannan shine na farko a rayuwar ta sa zatayi nesa da iyayenta,bata ta6ayin tafiya wani gari ba,hhhh sai kace ma chérie beauty Queen🤭
Sun sauka lafiya a garin bauchi,mai keke napep suka tara dan xuwa gida,
Da sukaje unguwar kai tsaye k'ofar gidanta tace da mai napep d'in ya kaisu,
Gidan a rufe alamar ba kowa,daman ita Allah bai bata haihuwa ba,daga ita sai mijinta,shima d'in ba wani mai kud'i bane amma dai yanada aikin yi,kuma suna cikin rufin asirin Allah,to alhmdllh,
Bayan sunyi wanka sun huta ne kanwar umma wacce suke kira da ammi tashi tayi ta shiga Kitchen don dora musu girki,
*HAMIDAH* tace''ammi ki kawo zanyi mana'',
''A,a 'yata ki barshi jeki zauna ki huta kinji ko,jelof kawai zanyi mana kafin a jima muyi wani abin'',
Babu yanda *HAMIDAH* batayi ba amma ta k'iya sai ta koma d'aki inda ammin ta nuna mata a matsayin nata ne,
Wayarta ce tayi k'ara sai da gabanta ya fad'i dan tasan mai Kiran,ita fa wlhy har yanxu bataji tanason yaya JAMIL ba,kawai dai ya cika nacin tsiya ne,hmm ai fa
D'auka tayi ta kara a kunne tare da yin sallama,daga can ya amsa mata,
''Babyta ya kike ne,da fatan kun isa bauchi lafiya?",
Cikin muryarta mai sanyi tace''lafiya lau'',
''To yayi kyau naji dad'i sosai da naji muryarki,nima da an kwana biyu zan leqo wajen naki'',
Ido ta zaro😳kamar yana ganinta''kai a,a dan Allah karkazo wlhy ammi na bata san da zancen nan ba,ita fa kawo ni tayi dan incigaba da karatu na,kasan babu dad'i ta ganni ina hira da saurayi,
''To babyta meye abin tsorata haka nan,zan hak'ura har lokacin da kika amince min koh?",bata amsa mishi ba,ya k'ara cewa''to tunda bazakiyi magana ba zan kashe saï anjima'',to kawai tace ta kashe daman duk a tsorace take kar ammi ta juyo su,hmm
********** *****
Zaman ta a gidan lafiya lau ba tsangwama bare takura suna waya da 'yan gida,umman ta ta tambayeta har ina ta samu waya sai ta bata hak'uri tace da zasu taho ne yaya JAMIL ya bata,
To umman dai ta gargad'eta sosai duk da dai ta yadda da tarbiyar 'yar tata,
Bayan wasu lokuta ne mijin ammin nata ya sama mata makaranta ta cigaba da tafiya skull,wannan kenan.....
Tafiya tayi tafiya,tun dai *HAMIDAH* na share JAMIL sai kawai kwatsam ta fad'a *tarkon so*,taji a duniya babu Wanda take k'auna irin JAMIL,toh🤔
Wata rana da yamma tana cikin d'akinta suna hira da JAMIL a waya yana ta zuba mata kalaman soyayya dan ya iya su sosai ya iya saye zuciyar mace,
Ita kuma sai shagwa6a take zuba mishi kamar tana gabanshi,kai abin zai baku mamaki wai yau *HAMIDAH* ce ke hirar soyayya har da k'yak'yatawa,
Batasan duk abinda takeyi ammi na tsaye ba,sai bayan sunyi sallama da habeebyn nata ne sannan ta juyo,ai kuwa sukayi ido 4 da ammin,wata irin fargaba ta shige ta........





0 comments:
Post a Comment